Hukuncin kotun koli: Allah ne kadai zai iya kwatan Najeriya – Uche Secondus

Hukuncin kotun koli: Allah ne kadai zai iya kwatan Najeriya – Uche Secondus

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus, a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, ya ce koda dai kotun koli ta yi watsi da karar da jam’iyyar da dan takararta na Shugaban kasa suka shigar, akan nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, hukuncin karshe na zuwa daga Allah ne.

Ya bayyana cewa kasar Najeriya na cikin wani hali da Allah ne kadai zai iya fitar da ita.

Ya yi magana ne a wani jawabi daga hadiminsa, Ike Abonyi, yayinda yake martani ga hukuncin da kotun kolin ta yanke na Koran karar da suka daukaka akan nasarar Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben ranar 29 ga watan Fabrairu.

Ya bukaci yan Najeriya da su cigaba da mika kukansu ga Allah, inda ya kara ce cewa kasar na cikin wani irin yanayi da sai Allah ne kadai zai iya fidda ta.

Secondus ya yaba ma yan Najeriya akan jajircewarsu da gudunmawar da suka ba jam’iyyar da damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Kwande na so Buhari ya roko malamai Larabawa daga kasar Saudiyya

Ya kuma yaba ma yan jarida akan jajircewarsu wajen damokradiyya da shugabanci nagari a Najeriya sannan ya bukaci da kada su yi kasa a gwiwa a rawar ganin da suke takawa don mutanen kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel