ASUU ta bawa gwamnatin tarayya sharadin shiga tsarin IPPIS

ASUU ta bawa gwamnatin tarayya sharadin shiga tsarin IPPIS

Kungiyar malamai masu karantarwa na jami'a, ASUU, ta sanar da Gwamnatin Tarayya cewa za ta koma tsarin IPPIS ne matukar Majalisar Dattawa ta gyara dokokin kafa jami'o'i.

Sauran sharuddan da kungiyar ta kafa sun hada da gyara a bangarorin zuwan malamai wasu jami'o'in da ba nasu ba don karantarwa, zuwa wasu jami'o'in da ba nasu ba don gwajin dalibai da kuma tattara alawus din duk malamin jami'a tare da fitar da sahihiyar shekarar da malaman na jami'o'in za su yi murabus.

Shugaban kungiyar, yankin jihar Sokoto, Dr. Jamilu Shehu, a karshen taron da hukumar tayi a Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina, ya ce, tsarin IPPIS ya rasa madogara ko makama ne daga kundin tsarin mulkin kasar nan sannan kuma babu wata dokar da take goyon bayansa daga majalisar dattawa.

DUBA WANNAN: Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Kamar yadda yace, kungiyar ba ta gamsu da tsarin IPPIS bane saboda ya sabawa dokokin da jami'o'in tarayya suka ginu a kai.

Ya kara jaddada cewa, yunkurin tilastawa malaman jami'o'in bin tsarin ba wai saba doka yayi ba kadai, ya hada da yin karantsaye ga yancin jami'o'in.

"Bayan haka, an yi karantsaye ga dokokin jami'o'in tarayya da suka bayyana cewa, hukumar gudanarwa ce ke da yanci akan duk wata wani bangare na kudin jami'a. IPPIS ta rasa goyon baya daga kundin tsarin mulki sannan kuma babu goyon baya daga wata dokar Majalisar Dattawa" in ji shi.

Ya ce: "ASUU shirye take da ta yi bore ga duk wata dokar da aka kirkiro don watsi da cigaban ilimi a kasar nan. Idan kuwa gwamnati ta dage akan tsayar mana da albashi saboda bamu shiga tsarin IPPIS ba, kungiyarmu za ta dau tsarin 'Ba biya, ba aiki"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel