Da duminsa: Alkalan Najeriya da INEC na da rauni - Atiku ya yi tsokaci kan faduwarsa

Da duminsa: Alkalan Najeriya da INEC na da rauni - Atiku ya yi tsokaci kan faduwarsa

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya yi tsokaci kan faduwar da ya samu a kotun kolin Najeriya a ranar Laraba, 30 ga Oktoba, 2019.

Kwamitin Alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Alkalin alkalai, Tanko Mohammed CJN, ta yi watsi da karar da PDP ta shigar saboda rashin abin azo a gani ciki.

Atiku ya bayyana bacin ransa da takaici kan yadda bangaren shari'a, yan jarida, da hukumar zabe ta INEC ba su da karfi a Najeriya.

Atiku ya ce wannan shari'a ya nuna cewa dukkan abinda PDP ta gina a shekaru 16 da tayi mulki na kawo cigaban demokradiyya, wannan gwamnatin ta rusa su.

A karshe ya mika godiyarsa ga yan Najeriya da suka nuna masa goyon baya da soyayya.

Yace: "A demokradiyya, ana bukatar bangaren shari'a mai karfi, yan jarida masu yanci da hukumar zabe mara ha'inci. Najeriya ba tada ko daya cikin wadannan a yau."

"Wannan shari'ar na daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a demokradiyyance."

Hakazalika, uwar jam'iyyar PDP ta bayyana kidimewarta da wannan shari'a inda tace abinda Alkalan su kayi ya sabawa zabin al'ummar Najeriya, har da yan jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel