Yanzu-yanzu: Buhari, APC sun yi tsokaci kan nasararsu kan Atiku da PDP

Yanzu-yanzu: Buhari, APC sun yi tsokaci kan nasararsu kan Atiku da PDP

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu kan nasarar da ya samu yau a kotun kolin Najeriya inda alkalan kotun sukayi watsi da karar jam'iyyar People’s Democratic Party PDP da dan takararta Atiku Abubakar.

Ya siffanta wannan nasara a matsayin karin tabbaci kan cewa yan Najeriya sun zabesa.

Yayinda yake magana da mai bada rahoton fadar shugaban kasa, Adamu Sambo, a Riyadh, kasar Saudiyya, Buhari ya yi alkawarin cigaba da kokarin da yake yi wajen kawo cigaba Najeriya.

Hakazalika, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yabawa watsi da karar PDP da Atiku da kotun koli tayi.

A jawabin da kakakin jam'iyyar Mallam Lanre Issa-Onilu, ya saki, ya ce: "Muna taya yan Najeriya; shugaban kasa, mataimakinsa, shugabannin jam'iyya, mambobi da masoya murnar wannan nasara ta kotun koli.

"Jam'iyyar tana yabawa Alkalan da tsayawa kan gaskiya duk da cin fuskar da PDP da Atiku ke yi musu ta hanyar tabbatar da niyyar al'ummar Najeriya da suka yanke shawarar fitittikan PDP da kuma sake zaben gwamnatin shugaba Buhari."

"Saboda haka, muna kira ga PDP da Atiku su daina ayyukansu na ganin karshen Najeriya duk da cewa sun yanke shawarar yin hakan a shekaru hudu masu zuwa."

Source: Legit

Tags:
Online view pixel