El-Rufai ya bayyana hanyar da ya bi don samun bashin $350m daga bankin duniya

El-Rufai ya bayyana hanyar da ya bi don samun bashin $350m daga bankin duniya

Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarar karbo bashin damin tamanin makudan kudade daga bankin duniya da suka kai dalan amurka miliyan 350 domin inganta ilimi a Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa El-Rufai ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wani taro a babban birnin tarayya Abuja inda suka taru don yin ban kwana ga daraktan ofishin bankin duniya dake Najeriya, Dakta Rachid Ben Massaoud.

KU KARANTA: Yadda fate fate ya halaka wasu yan biki guda 3, ya jikkata 2 a jahar Bauchi

Kungiyar gwamnonin Najeriya ce ta shirya ma Rachid wannan taro a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba, inda Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa akwai sama da makarantu 200 dake cikin mawuyacin hali a lokacin da dare mukamin gwamnan Kaduna.

“Na fuskanci babbar matsala, kuma ban san yadda zan yi dasu ba, idan kuma ban yi wani abu ba, yaran Kaduna zasu shiga mawuyacin hali. Don haka sai na dauki hotunan dukkanin makarantun, na hadasu a waje daya, daga nan sai na kai ma Ben Massaoud.

“Bayan ya ga hotunan sai ya tambayeni me nake so, ni kuma na fada masa cewa ina neman taimako ne, washegari ya gayyaceni domin mu tattauna hanyoyin da za’a bi domin shawo kan matsalolin ilimi a jahar Kaduna.” In ji shi.

Idan za’a tuna an sha kwaramniya game da batun amso wannan kudi a tsakanin Gwamna El-Rufai da kuma tsofaffin Sanatocin jahar da suka hada da Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma Sanata Danjuma La’ah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel