Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarkin Saudiyya, Salman (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarkin Saudiyya, Salman (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da sarkin masarautar Saudiyya, Sarki Salman, a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, a Riyadh, babbar birnin kasar.

A jiya, Shugaba Muhammadu Buhari ya fara halartan tarruruka a birnin Riyadh inda ya tattauna abubuwan da Najeriya ke bukata na sa hannun jari da kasuwanci.

Shugaba Buhari a ranar Talata ya halarci taro da sarkin Urdu, Abdullah na biyu, da firam ministan Indiya, Narenda Modi.

Kalli hotunan:

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarkin Saudiyya, Salman (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarkin Saudiyya, Salman (Hotuna)
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarkin Saudiyya, Salman (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarkin Saudiyya, Salman (Hotuna)
Source: Facebook

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

An fara taron ne daga ranar 29 ga wata kuma za'a kammala ranar 31 ga watan Oktoba, kuma za a tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

A cikin tawagar akwai karamin ministan harkokin kasashen waje, Zubairu Dada, ministan kamfanoni, kasuwanci da saka hannu jari, Niyi Adebayo, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, da ministan harkokin sadarwa, Dakta Ibrahim Pantami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel