Kwande na so Buhari ya roko malamai Larabawa daga kasar Saudiyya

Kwande na so Buhari ya roko malamai Larabawa daga kasar Saudiyya

- Tsohon jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Yahaya Kwande ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi amfani da damar ziyarar da ya kai kasar Saudiyya wajen roko malamai Larabawa

- Kwande yace hakan zai kara karfafa fahimtar addini a tsakanin yan Najeriya da kuma wanzar da zaman lafiya da fahimta a tsakanin al’umman kasar

- Hakan ya yi shige da wani roko da marigayi Sheikh Mahmud Gumi ya yi a shekarun baya

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Yahaya Kwande ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi amfani da damar ziyarar da ya kai kasar Saudiyya inda yake halartan taron tattalin arziki wajen neman gwamnatin Saudiyya ta turo malaman da za su koyar da harshen Larabci zuwa Najeriya.

Kwande yace hakan zai kara karfafa fahimtar addini a tsakanin yan Najeriya da kuma wanzar da zaman lafiya da fahimta a tsakanin al’umman kasar.

Ya kuma bayyana cewa: “Hakan zai age rikici idan yaranmu suka fahimci harshen Larabci da kyau, kuma zai taimaka masu wajen fahimtar addininsu sosai sannan kuma ta haka zai kara karfafa fahimtarmu akan abubuwa da yadda ya kamata mu zauna da sauran yan uwanmu daga addinai daban-daban."

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Kotun koli ta tsaya cak a kan karar Atiku da Shugaba Buhari

A wani roko makamancin haka da marigayi babban malamin musulunci, Sheikh Mahmud Gumi ya yi a shekarun baya, ya roki gwamnatin Saudiyya da ta yi amfani da albarkatun da Allah ya bata wajen daukar nauyin malaman addini domin su koyar da yan Najeriya harshensu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel