Yanzu -Yanzu: Atiku ya kara faduwa a kotun koli

Yanzu -Yanzu: Atiku ya kara faduwa a kotun koli

Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka yi wacce ke kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da ya gudana.

Kungiyar alkalan bakwai na babbar kotun da ta samu jagorancin Jastis Tanko Mohammed, shugaban alkalan Najeriya, ta ce, sun sakankance cewa babu wani amfani game da daukaka karar. A don haka ne suka yi fatali da karar..

DUBA WANNAN: Yanzu - Yanzu: Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Tambuwal

Shugaban alkalan Najeriya, Jastis Tanko, ya kara da cewa, kungiyar alkalan ta duba tare da yin nazari akan shari'ar tun kusan makonni biyu da suka gabata.

Ya ce, za a sanar da dalilin watsi da karar a ranar da kotun zata sanya.

Atiku da jam'iyyarsa na kalubalantar hukuncin ranar 11 ga watan Satumba ne wanda ya samu jagorancin Jastis Mohammed Garba a kotun sauraron kararrakin zabe. Karar kuwa na kalubalantar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a zaben shugabancin kasa da ya gabata.

Bayani zai biyo baya nan gaba kadan...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel