Ba ace mu fara biyan sabon mafi karancin albashi ba tukuna – DG NYSC

Ba ace mu fara biyan sabon mafi karancin albashi ba tukuna – DG NYSC

Mun ji Darekta Janar na hukumar NYSC, Birgediya-Janar Shuaibu Ibrahim ya bayyana halin da ake ciki a game da barun karin alawus game da Matasan da ke yi wa kasa hidima ta tsarin.

Janar Shuaibu Ibrahim ta sanar da Manema labarai cewa kawo yanzu bai samu wani izni daga Ministar kudi na cewa ya soma biyan masu bautar kasa N30, 000 kamar yadda aka kara albashi.

Shuaibu Ibrahim ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya zanta da Manema labarai a Ranar 29 ga Watan Oktoba. Ibrahim yace ya tabbata cewa masu aikin NYSC za su amfana da karin albashin.

NYSC ta bayyana wannan a jiya Talata jim kadan bayan kaddamar da wani babban taron da hukumar ta shirya tare da wakilan gwamnonin jihohi. Ana taron ne a babban birnin tarayya.

KU KARANTA: Ministan Matasa ya yi fushi wajen taron NFF a Abuja

Janar din yake yi wa Manema labarai karin bayani cewa daga cikin hakkokin masu aikin NYSC a kan gwamnatocin jihohi da kananan hukuma shi ne a ba su wurin kwana da filin noma da tsaro.

Darekta Janar din na hukumar NYSC yake cewa sashe na 7 da na 8 na dokokin NYSC sun yi bayani dalla-dalla a game da nauyin gwamnatoci ga matasan da ke aikin bautawa kasarsu.

Gwamnatin tarayya ce ta ke daukar mafi yawan nauyin tsarin inda ta ke da alhakin ciyarwar Matasan da kuma kula da lafiyarsu, tare da biyansu alawus duk wata da dai sauransu.

Kamar yadda aka tabbatar da karin albashin ma’aikatan gwamnati, Ministan matasa ya bada tabacin cewa za a kara alawus din da ake ba matasan da ke bautar kasa na tsawon shekara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel