Zaben 2019: Kotun koli ta tsaya cak a kan karar Atiku da Shugaba Buhari

Zaben 2019: Kotun koli ta tsaya cak a kan karar Atiku da Shugaba Buhari

Sauraron shari’an da dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya shigar a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, ya samu tsaiko daga kotun koli.

Legit.ng ta fahimci cewa kwamitin mutum bakwai wanda Shugaban alkalan Najeriya, Tanko Mohammed ke jagoranta sun yanke wannan shawarar ne domin ba lauyan Atiku, Levy Uzokwu (SAN), damar yanke shawara akan tsarin sauraron karar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun kolin na son yanke hukunci ta hanyar fitar da matsaya daya tal a shari'ar zaben Shugaban kasar akan ainahin karar sannan hakan zai shafe duk sauran.

Rahoton yace Wole Olanipekun, Ustaz YYinusa da Lateef Fagbemi, wadanda ke tsaya ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), duk sun amince da wannan matsaya na kwamitin.

Sai dai kuma, wannan mataki sam bai yiwa lauyan Atiku ba.

"Idan kana son lokaci domin yanke shawara, za mu baka lokaci. Ba ma so ka je ka rubuta wani kara akanmu daga baya cewa mune muka tursasa ka yanke shawara," Justis Tanko ya fada ma Uzokwu.

KU KARANTA KUMA: APC ta ki amince wa da yunkurin shigo da shinkafa mai araha daga wata kasar waje

An tattaro cewa ainahin lamarin dake cikin sauran kararrakin shine soke wasu layuka da kotun zaben shugaban kasa ta yi a cikin karar Atiku da PDP.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel