Yanzu - Yanzu: Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Tambuwal

Yanzu - Yanzu: Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Tambuwal

Kotun daukaka kara ta jihar Sokoto, ta kwace kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Sokot ta kudu, Abubakar Tambuwal na jam'iyyar APC. Ta bada umarnin maye gurbinsa da dan takarar jam'iyyar PDP, Ibrahim Danbaba.

Dan takarar PDP, Ibrahim Danbaba, ya daukaka karar ne domin kalubalantar nasarar Tambuwal a kotun sauraron kararrakin zabe da ta jaddada nasarar Tambuwal din.

Yayin yanke hukunci a ranar Laraba a kotun daukaka karar, mai shari'a Federich Oho, ya ce Danbaba yayi nasarar daukaka karar a don hakane yake umartar da ya maye gurbin Tambuwal.

DUBA WANNAN: Yanzu - Yanzu: CJN Tanko ya bayyana alkalan da zasu saurari daukaka kara Atiku a kotun koli

Zamu iya cewa cikin kwanakin nan, 'yan jam'iyyar APC sun tsinci kansu cikin mawuyacin hali a yawancin shari'un da akeyi. Domin kuwa ana ta maka su da kasa a kotu.

Sabon abinda ya samu jam'iyyar a jihar Sokoto kuwa shine hukuncin kotun daukaka kara da ta umarnin a yi sabon zaben mazabar tarayya ta arewacin Sokoto da Kudancin Sokoto, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel