Sunday Dare ya ki ganawa da Amaju Pinnick da Shehu Dikko saboda makara wajen taro

Sunday Dare ya ki ganawa da Amaju Pinnick da Shehu Dikko saboda makara wajen taro

Ministan cigaban Matasa da wasannin Najeriya, Sunday Dare ya fice daga wajen taro ya kyale manyan kusoshin harkar kwallon kafan kasar saboda sun zo wajen taron a makararren lokaci.

An shirya zama ne tsakanin shugaban hukumar kwallon kafan Najeriya Amaju Pinnick da mataimakinsa Shehu Dikko da kuma Ministan wasannin kasar, Sunday Dare a filin wasan Abuja.

A ka’ida ya kamata a soma wannan ganawa ne da karfe 4:00 na yamma. Har lokacin da aka sa zaman a babban filin wasan na MKO Abiola ya yi, Mai girma Ministan ne kurum ya iya isa wurin.

Ganin wadannan jami’ai ba su hallara ba, Ministan ya kama hanya zai fice abinsa. A hanyarsa ta fita na ya ci karo da shugaban na NFF, Amaju Pinnick, wanda ya yi kokarin yi masa wasu bayanai.

KU KARANTA: 'Yan wasan da ba su taba samun damar bugawa Super Eagles ba

Daily Trust tace bisa dukkan alamu, Ministan ya fusata da abin da ya faru inda ya ki sauraron abin da Amaju Pinnick ya ke kokarin fada masa a matsayin dalilin da ya sa su ka makara.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta mata, Aisha Folade ta na cikin wadanda aka shirya za ayi wannan zama da su. Dukkansun dai sun iso ofishin taron ne da kimanin karfe 4:20 na yamma.

Jim kadan bayan Ministan ya bar wurin, an rahoto Mista Amaju Pinnick wanda yake a gigice, ya na cewa: “Makarar minti goma kurum mu kayi, a kan me Ministan zai tafi ya kyale mu haka?”

Daga bayan dai shugabannin sun hadu. Amma dama can ana rade-radin sabon Ministan ya dade yana hakuri da shugaban na NFF din wanda ba ya ganin girman darajar kujerar Maigidansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel