KAI TSAYE: Yadda shari'ar kotun koli tsakanin Buhari da Atiku ke gudana

KAI TSAYE: Yadda shari'ar kotun koli tsakanin Buhari da Atiku ke gudana

Lauyan PDP, Livy Uzuokwu ya fara gabatar da jawabinsa, ya yi magana kan abubuwa uku

1. Babu hujjan cewa sunan Mohamed, Muhammad da Muhammadu daya ne kamar yadda Alkali Garba ya yanke

2. Buhari bai gabatar da takardar 'Testimonial" daga makarantar da yayi ikirarin cewa ya halarta ba. Saboda haka babu hujjan cewa Buhari ya je makarantar sakandare

3. INEC ta jahilci sabon dokan da ya bata daman tura sakamakon zabe ta yanar gizo

Muna kawo muku rahotanni kai tsaye kan yadda kotun kolin Najeriya karkashin jagorancin shugaban Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko, ke zaman shari'a kan hukuncin kotun daukaka kara da tayi watsi da karar Atiku a watan jiya.

Kotun koli ta nada kwamitin Alkalai bakwai da zasu saurari jawaban lauyoyin APC, PDP, INEC, Buhari da Atiku kafin yanke hukunci.

Mambobin sune:

Tanko Mohammed

Bode Rhodes-Vivour,

Amiru Sanusi,

Uwani Abaji,

Ejembi Eko,

John Inyang Okoro

Olukayode Ariwoola

A yanzu shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, da babban jigon APC, Nuhu Ribadu; shugaban PDP, Uche Secondus da jigon PDP, Raymond Dokpesi na hallare a kotu

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel