APC ta ki amince wa da yunkurin shigo da shinkafa mai araha daga wata kasar waje

APC ta ki amince wa da yunkurin shigo da shinkafa mai araha daga wata kasar waje

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba, ta yi watsi da bukatar kasar Vietnam na shigo da shinkafa mai araha cikin Najeriya.

Jam’iyyar ta APC ta ce amincewa da bukatar zai cigaba da illata tattalin arzkin kasar.

Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin wata tawaga karkashin jagorancin mataimakin Firai ministan kasar Vietnam, Vuong Hue, a Abuja.

Hue, wanda ke shirin haduwa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a yau Laraba, ya nemi taimakon jam'iyya mai mulki kan a bari kasar ta shigo da shinkafa mai sauki cikin Najeriya.

Amma Oshiomhole ya ce: "Idan gwamnati ta bari aka shigo da abinci daga waje, matasanmu za su zauna babu abun yi, hakan zai yi sanadiyar rashin aiki. Muna so mu inganta tsaron abinci.

"Maimakon shigo da shinkafa daga Vietnam, manoman kasarku na iya amfani da damar filayenmu masu albarka. Ya zama dole mu yi hakan ba wai don kare manomanmu ba kawai sai don magance tsaron abinci."

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An tsare wani malamin addini kan satar talotalo da akuya

Oshiomhole yace hukuncin rufe iyakokin kasar da gwamnatin tarayya ta yi ya cancanci samun goyon bayan duk wani dan Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel