Yanzu - Yanzu: CJN Tanko ya bayyana alkalan da zasu saurari daukaka kara Atiku a kotun koli

Yanzu - Yanzu: CJN Tanko ya bayyana alkalan da zasu saurari daukaka kara Atiku a kotun koli

Shugaban alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Mohammed ne zai shugabanci kungiyar alkalai 7 da zasu saurari daukaka karar da PDP da dan takararta Atiku Abubakar suka yi akan kalubalntar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 23 na watan Fabrairu, 2019.

Sauran alkalan da ke kungiyar sun hada da: Bode Rhodes-Vivour, Amiru Sanusi, Uwani Abaji, Ejembi Eko, John Inyang Okoro da Olukayode Ariwoola. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Atiku da jam'iyyarsa suna kalubalantar hukuncin ranar 11 ga watan Satumba ne da Jastis Mohammed Garba ya jagoranta a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa. Hukunci kuwa ya jaddada nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a zaben shugabancin kasa da ya gabata.

DUBA WANNAN: Wata cuta ta barke a jihar Katsina, ta lashe rayukan mutane da dama

Sauraron daukaka karar ya jawo cece-kuce daga jam'iyyun adawa ganin cewa kotun kolin tayi shiru akan maganar alkalan da zasu saurari karar.

A jiya da wakilin jaridar Daily Trust ya zanta da daya daga cikin manyan lauyoyin Atiku, Chief Chris Uche, ya ce , abin yayi musu banbarakwai saboda har a lokacin, wanda ya daukaka karar bai san alkalan da zasu saurari shari'ar ba.

A bangaren daya daga cikin lauyoyin kuwa Buhari, Dr Alex Izinyon, ya ce, kungiyarsu bata bukatar sanin alkalan da zasu saurari shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel