Hujojji da muke da su za su bamu nasara a kotun koli, PDP ta fadawa APC

Hujojji da muke da su za su bamu nasara a kotun koli, PDP ta fadawa APC

Jam'iyyar PDP ta ce, shaidu da hujjoji da ta mallaka ne za su bata nasara a kan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a kotun koli.

Kamar yadda sakataren yada labarai na jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya jaddada cewa, suna da shaidu gamsassu da suka tabbatar da Atiku Abubakar ne yayi nasara a zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Jam'iyyar ta PDP ta ja kunnen APC da masu goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da su guji bacin suna ko zargi marasa tushe gareta da kuma Atiku Abubakar, ganin cewa ba zasu tsallake a shari'ar kotun kolin ba.

DUBA WANNAN: A wajen kananan yara nake samun gamsuwa, in ji wani dan luwadi

PDP tace, ganin karfin shaidun da ake dasu sun isa tunkude shugaban kasa Muhammadu Buhari daga karagar mulkin, yasa APC ke kirkiro labarai da barazana kala-kala.

"A yunkurin kawar da hankalin kotun kolin, sun tattara duk abubuwan da zasu batawa PDP suna da su"

Sakataren ya kara da cewa, "PDP na da kwakwarar kara a kotun kolin. Tana tare da 'yan Najeriya ne da kuma yardar cewa za a yi adalci. A dayan bangaren kuma, ganin cewa babu nasara ga APC, ta fara kirkiro makirci kala-kala don ganin sun hana adalcin."

"Yan Najeriya na sane da yadda APC ta koma bayan da suka ga PDP da Atiku Abubakar sun mallaki shaidun da ba za a musa ba a gaban kotun kolin. Hakan kuwa ya hada da rashin adalcin da aka nuna a kotun sauraron kararrakin zaben wacce ko ita kotun tasan akwai kura-kurai masu yawa a hukuncinta." In ji PDP

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel