Majalisa wakilai ta nuna rashin amincewa da sabon shirin rundunar soji na ‘operation positive identification’

Majalisa wakilai ta nuna rashin amincewa da sabon shirin rundunar soji na ‘operation positive identification’

Mambobin majalisar wakilai sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu da ya datse aikin sojoji na operation positive identification da ake shirin farawa.

A wani muhawara da Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Ndudi Elumelu ya gabata a matsayin abu da ke bukatar kulawar gaggawa, dan majalisar ya nuna damuwa kan cewa shirin zai sanya tsoro a zukatan yan Najeriya.

Batun ya kuma nuna cewa aikin zai tubewa yan Najeriya yancin da kundin tsarin mulki ya basu na zirga-zirga sannan ya sanya masu tsoro, fargaba da kuma tashin hankali a hakokinsu, inda ya kara da cewa aikin na fadin kasa baki daya a fakaice zai zama tamkar sojoji sun sanya dokar ta baci ne a fadin kasar.

A nasu gudunmawar, wasu yan majalisa sun bayyana cewa yin hakan hakkin yan sanda ne amma ba wai na sojoji ba.

KU KARANTA KUMA: Mutuwar mai laifi: Jarumin dan sanda Abba Kyari ya shiga tsaka mai wuya

Kwamitin majalisar kan rundunar soji za ta gana da Shugaban hafsan soji domin kara fahimtar nufin aikin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban hafsun Sojin kasan Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, ya amince da sauyi da nadin mukaman aikin da su ka shafi wasu Manjo Janar 5 da Birgediya Janar 4 na Najeriya.

Kamar yadda mu ka ji labari daga bakin Mukaddashin Darektan sojojin na hulda da Jama'a, Kanal Sagir Musa, daga cikin Sojojin da aka canzawa wurin aiki akwai Manjo-Janar Jamil Sarham.

Sagir Musa ya bayyana wannan ne a jawabin da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja Ranar 29 ga Watan Oktoba. Manjo-Janar F.O Agugo ya zama sabon GOC na shiyya ta shida da ke Fatakwal.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel