Rufe iyakokin da Najeriya ta yi, zai kawowa ECOWAS cikas – Nana Addo

Rufe iyakokin da Najeriya ta yi, zai kawowa ECOWAS cikas – Nana Addo

A karon farko, shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana ya tofa albarkacin bakinsa game da matakin da Najeriya ta dauka na rufe kan iyakokinta da Makwabciya Benin.

Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bayyana garkame kan iyakokin Najeriya da aka yi a matsayin cikas ga tsarin zaman taren da ake yi a yankin. Wannan ne dai karon farko da Ghana ta yi magana.

A Ranar 29 ga Watan Oktoba, Shugaba Nana Addo ya ce wannan mataki da aka dauka ya na iya bata zaman da ake yi. Addo ya yi wannan bayani ne a lokacin ya karbi bakuncin shugaban bankin First Bank.

Shugaba Akufo-Addo ya fadawa wadanda su ka kai masa ziyara har fadar shugaban kasa na Jubilee House da ke Garin Accra da ke Ghana cewa: “Mu na neman shiga wani lokaci a tafiyar ECOWAS.”

KU KARANTA: 'Yar kasar waje ta yi amfani da sunan Najeriya ta damfari wani

Jawabin shugaban ya cigaba: “A daidai lokacin da mu ke duba yiwuwar kirkiro kudi guda tare da dunkule tattalin arzikin kasashemu, game da kuma matsalar tsaron da ke damun a wannan lokaci…”

“…Sai ake maganar rufe iyakar Benin wanda ya kasance ci-baya game da shirin ECOWAS.” Shugaban yace bai kamata wata kasa ita kadai ta yi abin da ta ga dama, ta yi watsi da ‘yanuwan ta ba..."

“Ina ganin akwai wasu abubuwa da ya kamata mu duba domin mu samu hanyar da za mu zauna cikin kwanciyar hankali a wannna yanki, kuma mu tabbatar da cikar burin kowace kasa cikinmu.”

A jawabin na shugaban kasar, ya nuna cewa ana sa rai abubuwa su dawo daidai a sakamakon zaman da ake yi tsakanin wakilan manyan kasashen biyu na Nahiyar Yammacin Afrika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel