Wata cuta ta barke a jihar Katsina, ta lashe rayukan mutane da dama

Wata cuta ta barke a jihar Katsina, ta lashe rayukan mutane da dama

Barkewar wata cutar da ake zargin 'shawara' ce ta lashe rayukan mutane da yawa a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina. Mazauna yankin sun ce wadanda suka mutu sun kai mutane 115 inda gwamnatin karamar hukumar ta ce mutane 18 kacal ne suka rasu a cikin makonni uku da suka gabata.

Tsohon kansilan gundumar Kogware, Malam Sule Ibrahim, ya ce, an fara samun barkewar cutar ne a gundumar Kogware kafin ta isa Unguwar- Sarka.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Kotu ta kara kwace kujerar APC a jihar Sokoto

Ya ce, "A cikin makonni uku da suka shude, mun kirga rashe-rashe na mutane 112 tare da karin mutane 3 a cikin ranakun karshen makon nan."

Amma kuma da aka tuntubi sakataren cibiyar lafiya ta yankin, Dr Shamsu Ahmad, ya ce "Ana zargin cutar shawara ce. A lissafinmu, mun samu rahoton mutane 45 da suka kamu da cutar inda 18 suka rasu."

"A yau ranar Litinin, mun samu jimillar mutane 45 da suka zo da cutar. An dauka jinin mutane 11 daga ciki. Sakamakon ya nuna biyar daga ciki ba cutar shawara bace, muna jiran sakamakon mutane 6. Muna kai jinin Abuja ne don yin gwajin, sakamakon rashin kayan aiki a nan din," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel