An yi musayar yawu da nuna ma juna yatsa tsakanin daliban da aka sace da Yansandan Kaduna

An yi musayar yawu da nuna ma juna yatsa tsakanin daliban da aka sace da Yansandan Kaduna

Cacar baki ya kaure tsakanin wasu dalibai 6 da yan bindiga suka yi garkuwa dasu a garin Kaduna, tare da iyayensu a bangare guda, da kuma hukumar Yansandan jahar Kaduna a bangare guda a kan gaskiyar yadda yaran suka kubuta daga hannun miyagun.

Jaridar Punch ta ruwaito iyayen yaran sun musanta ikirarin da rundunar Yansandan jahar Kaduna ta yi na cewa wai ita ta ceto yaran daga hannun yan bindigan, inda iyayen suka ce kudin fansa suka biya aka sako musu yaransu.

KU KARANTA; Ba sani ba sabo: Jami’an EFCC sun yi dirar mikiya akan manyan jami’an hukumar zabe INEC

A ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 2019 yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai 6 da malamansu guda biyu daga wata makarantar sakandari mai suna Engravers dake Kakau Daji cikin karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sai a ranar Asabar din data gabata aka sako yaran bayan kwashe kimanin kwanaki 23 a hannun yan bindigan tare da biyan kudi naira miliyan 13.6. amma a hannu guda kuma, Yansanda sun yi ikirarin ceto yaran da malamansu bayan samun bayanan sirri.

Cikin wata sanarwa da kaakakin Yansandan Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya fitar a ranar Asabar, yace:

“A yau 26 ga watan Oktoban 2019 da misalin karfe 8 jami’anmu na Operation Puff Adder dake Kaduna sun kwato dalibai da malaman makarantar Engravers bayan samun bayanan sirri. Da haka muka kubutar da dukkanin mutanen su 8, kuma mun mikasu ga iyalansu.”

Sai dai iyayen yaran sun musanta ikirarin Yansanda, inda wakilinsu, Ohemu Fredrick ya bayyana ma manema labaru a ranar Talata cewa yan bindigan ne suka saki yaran bayan an biyasu kudin fansa, sa’annan ya kara da cewa akwai wani tsohon gwamnan Kaduna daya taimaka musu da makudan kudade.

Haka zalika Ohemu yace wannan tsohon gwamna ya taimaka musu wajen daukan nauyin kulawa da yaran a asibiti tare da malamansu.

Shi ma wani daga cikin iyayen yaran ya bayyana cewa sai da yan bindigan suka sako yaran, bayan yaran sun fito bakin titi ne sai suka hadu da Yansanda, daga nan Yansandan suka daukesu a motarsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel