Yau za a fara sauraron karar Shugaba Buhari da Atiku a kotun koli

Yau za a fara sauraron karar Shugaba Buhari da Atiku a kotun koli

Alkalan Kotun kolin Najeriya za su fara sauraron karar da Atiku Abubakar ya daukaka a game da shari’ar zaben shugaban kasa. ‘Dan takarar jam’iyyar hamayyar ya na kalubalantar nasarar APC.

Lauyoyin Alhaji Atiku Abubakar su na ikirarin cewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ba ne ya lashe zaben 23 ga Fubrairun bana. Kotun farko ta yi fatali da wannan.

Bayan Atiku Abubakar ya rasa karar da ya shigar a gaban kotun da ke sauraron korafin zabe, PEPT, ya dumfari babban kotun kasar da nufin ganin an rusa nasarar da shugaba Buhari ya samu.

Yayin da ake shirin fara shari’ar a Yau Laraba, 30 ga Watan Oktoba, har yanzu babu wanda ya san Alkalan da aka zaba a kotun kolin domin su karbi korafin da Lauyoyin Abubakar su ka shigar.

KU KARANTA: APC ta rasa kujerar Majalisar Sokoto a gaban kotun zabe

Kungiyar CUPP ta hadakar ‘yan hamayya tace a bi girma wajen zaben Alkalan da za su yi shari’ar. Lauyan Atiku Chris Uche ya ce gum din da aka yi na kin bayyana masu shari’ar bakon abu ne.

Uche wanda ya na cikin manyan masu kare 'Dan takarar PDP ya nuna su na sa ran samun nasara a gaban babban kotun, ganin irin tarin hujjojin da su ka gabatar a gaban karamin kotu a baya.

Ra’ayin wani babban Lauyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dr. Alex Izinyon ya sha banbam da na Kungiyar CUPP ta jam’iyyun hamayya inda yace ba su bukatar sanin masu shari’ar.

Wannan sauraron daukaka kara ya na zuwa ne kusan wata guda kenan bayan Lauyoyin Atiku Abubakar na PDP sun koma kotu a dalilin rashin gamsuwarsu ga hukuncin da aka yi a Satumba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel