Wata 'yar kasar Malaysiya tayi amfani da sunan Najeriya ta damfari Bature makudan kudade

Wata 'yar kasar Malaysiya tayi amfani da sunan Najeriya ta damfari Bature makudan kudade

- An kama wata mata 'yar kasar Malaysiya da take zaune a kasar Amurka da laifin damfara

- An kama matar tayi amfani da sunan wani kamfani na karya da sunan Najeriya

- Haka kuma an bayyana cewa matar tayi amfani da sunayen kusan mutane shida wajen boye kowacece ita

Wata mata 'yar kasar Malaysia mai suna Siew Im Cheah dake zaune a kasar Amurka an yanke mata hukuncin watanni 51 a gidan yari bayan ta damfari wani jami'in gwamnatin birnin Virginia dala dubu dari uku da sunan Najeriya.

Wannan labari dai mun kawo muku shine kamar yadda jaridar Washington Times ta ruwaito a ranar Litinin 27 ga watan Oktoba.

Wata mata 'yar kasar Malaysia da take zaune a kasar Amurka ta damfari wani jami'in gwamnatin kasar Amurka makudan kudade ta hanyar tura mata kudi a wani kamfani da ta bude na Najeriya na karya.

Siew Im Cheah mai shekaru 51 ta yaudari Jimmy Rhee, wanda a lokacin jami'in gwamnatin birnin Virginia ne, inda ta bayyana masa cewa tana da hanya da wani kamfanin man fetur har ta yaudare shi ya tura mata dala dubu dari uku.

KU KARANTA: Wanda ya mutu ya mutu, dan haka ba dole ne sai na halarci jana'izar mahaifiyata ba - Nnamdi Kanu

Mai gabatar da kara ya bayyana cewa Cheah ta yi amfani da kimanin sunayen mutane shida, wanda suka hada da abokiyar zamanta da dai sauran su. An bayyana cewa ta kashe kudin ne wajen sayen manyan motoci da jakankuna masu tsada.

A farkon shekarar ne Cheah ta shiga kasar Amurka a matsayin wacce taje yawon bude ido, an kuma kama ta da laifin gudu a cikin wata mota da kuma amfani da lasisin tuki na kawarta, yanzu dai an tura ta gidan yari a ranar 4 ga watan Oktobar nan na tsawon watanni 51.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel