EGRP: Mu na neman Dala Tiriliyan uku a cikin shekaru 30 – Zainab Ahmed

EGRP: Mu na neman Dala Tiriliyan uku a cikin shekaru 30 – Zainab Ahmed

Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed, ta ce Najeriya na bukatar makudan dukiya masu yawa domin dabbaka shirin EGRP da zai habaka tattalin kasar.

Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa tsarin EGRP da sauran manufofin da gwamnatin tarayya ta kawo domin ganin an babbako da tattalin arziki su na fuskantar matsalar rashin kudi.

Ministar ta yi wannan bayani ne a Ranar Talata a birnin tarayya Abuja, yayin da ta ke magana wajen taron wani kwamiti da ke aiki a kan batun kudin-shiga a karkashin kungiyar gwamnoni.

Misis Ahmed ta ke cewa tun a shekarar 2017 Najeriya ta ke fama da karancin kudin shiga na IGR. A wannan shekarar ne gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirin ERGP.

KU KARANTA: Mutumiyar Najeriya ta samu mukami a majalisar dinkin Duniya

A cewar Ministar, rashin samun isasshen kudin da gwamnatin ta ke buri, ya jawo aka rika kaucewa manufar ERGP da ake sa ran zai tada tattalin arzikin Najeriya wanda ya ruguje a baya.

Wannan sakin layi da aka rika yi ya na tasiri a kan tattalin arzikin kasar kamar yadda Ministar ta bayyana. Ministar ta yi duk wannan jawabi ne ta bakin Darektan ma’aikatarta, Dr. Israel Igwe.

Darektan yace: “Najeriya ta na bukatar kudin da za su fito ta harajin ta, domin ta zauna da kafafunta. Mu na bukatar Dala tiriliyan uku domin magance matsalolin abubuwan more rayuwa.”

Igwe ya kara da cewa: “Gazawar gwamnati na karbar haraji daga sauran bangarori ban da na man fetur ya fito fili. Abin da mu ka iya samu a 2019 a Watan Yuni, kashi 42% na abin da mu ke hari ne.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel