Ba sani ba sabo: Jami’an EFCC sun yi dirar mikiya akan manyan jami’an hukumar zabe INEC

Ba sani ba sabo: Jami’an EFCC sun yi dirar mikiya akan manyan jami’an hukumar zabe INEC

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun yi dirar mikiya a babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na INEC reshen jahar Sakkwato a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa jami’an na EFCC sun yi awon gaba da wasu manyan jami’an hukumar INEC domin su amsa muhimman tambayoyin da EFCC ta shirya musu.

KU KARANTA: Dakarun Sojan ruwa sun kwato dabbobi 318 mallakin Fulani daga hannun barayi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu jami’an ofishin INEC dake jahar Sakkwato sun tabbatar da kamen, sai dai basu yi karin bayani game da yanayin laifin da ake tuhumar da jami’an da aka yi awon gaba dasu ba, sakamakon basu da izinin yin magana da yan jaridu.

Idan za’a tuna a yan kwanakin bayan nan ne hukumar EFCC reshen jahar Sakkwato ta kama wasu jami’an INEC guda hudu a kan laifin karkatar da kudi naira miliyan 84.6 hakkokin ma’aikatan da suka gudanar da zaben 2019 da suka ki biyansu.

Kaakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana cewa EFCC ta kama mutanen ne sakamakon kara da wani Abdullahi Nasiru ya shigar gabanta a madadin kafatanin ma’aikatan zaben wucin gadi da suka gudanar da zaben 2019 a jahar Zamfara.

Sai dai wasu ma’aikatan wucin gadin sun tabbatar da cewa sun fara samun kudadensu da sanyin safiyar Talata 29 ga watan Oktoba ta asusun ajiyan kudadensu na banki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel