Wani direban mota ya kashe dan KAROTA a Kano

Wani direban mota ya kashe dan KAROTA a Kano

Wani ma'aikacin hukumar kula da cunkuson ababen hawa da aka fi kira da suna 'KAROTA' a Kano ya mutu ranar Talata bayan wani direba ya take shi da mota.

Ma'aikcin mai shekaru 27 ya rasa ransa ne akamakon buge shi da mota da wani direba ya yi a daidai lokacin da yake kokarin kama shi saboda ya ki tsaya wa a lokacin da danja ta tsayar da masu tafiya a titin da yake kai.

Lamarin ya faru ne a kan titin zuwa filin jirgin sama na Kano, kamar yadda rahotanni daga birnin Kano suka tabbatar wa da majiyar Legit.ng.

Kakakin hukumar KAROTA, Nabulisi Abubakar Kofar Na'isa, ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin tare da bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan direban ya tsaya a hanyar zuwa ofishin jami'an KAROTA bayan sun kama shi da laifin karya dokar tuki.

DUBA WANNAN: Wata cuta ta barke a jihar Katsina, ta lashe rayukan mutane fiye da 100

Tsayawar da direban motar ya yi ne yasa jami'in na KAROTA mai suna Tijjani Adamu ya fito daga motarsu ta ma'aikata domin ya kwance lambar motar da direban ke ciki bayan ya tsaya, ya ki motsa wa gaba ko baya.

Kakakin ya kara da cewa marigayi Adamu ya yi kokarin kwance lambar motar mutumin, lamarin da yasa shi kuma ya zaburi motar, inda nan take ya buge jami'in tare da taka shi, sannan kuma ya gudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel