Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Abba Moro

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Abba Moro

Kotun daukaka kara da zaman ta a Makurdi, a ranar Talata ta tabbatar da nasarar Kwamared Abba Moro a matsayin Sanata mai wakiltan mazabar Binuwai ta Kudu.

Alkalin kotun, Mai shari'a Jumai Sankey, ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron karrakin zabe na jihar ta yanke na bawa Moro nasara kan karar da abokin fafatawarsa Cif Stephen Lawani na jam'iyyar APC ya shigar na kallubalantar nasararsa.

Mai shari'a Sankey ta yi watsi da karar da aka shigar na kallubalantar Moro na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kan cewar babu wasu kwararran hujojji.

DUBA WANNAN: Wani mutum ya 'mutu' ya dawo bayan shekara 30 a Kano

Kotun daukaka karar ta kuma umurci wadanda suka shigar da karar su biya kudi har N200,000.

A baya, Daily Trust ta ruwaito cewa kotun sauraron karrarkin zabe karkashin jagorancin mai shari'a A A Adeleye, a watan Satumba ta yi watsi da karar da aka shigar a kan Moro inda ta ce wanda ya shigar da karar ga gaza gabatar da kwararran hujojji da za su tabbatar da zargin da ya gabatar.

Kotun zaben ta ce mafi yawancin hujojjin da wanda ya shigar da karar ya gabatar an gina su ne kan 'jita-jita' kuma kotu ba ta aiki da jita-jita.

Adeleye ya kuma ce wanda ya shigar da karar da jam'iyyarsa ta APC sun gaza gabatar da kwararran hujjoji kan zargin saba dokokin zabe da suka ce an yi don dukkan shaidan da aka gabatar ba su gamsar da kotun ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel