Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattijai kan nada mambobin hukumar NDDC (Sunaye)

Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattijai kan nada mambobin hukumar NDDC (Sunaye)

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattijai wasika a kan naman tabbatar da mambobin majalisar hukumar Cigaban Neja Delta (NDDC).

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanto wasikar a yayin zaman majalisar na ranar Talata 29 ga watan Oktoba.

Wadanda aka zaba a matsayin mambobin majalisar ta NDDC sune Ciyaman, Pius Odubu (Edo); Manajin Direkta, Bernard O. Okumagba (Delta); Direktan Ayyuka, Otobong Ndem (Akwa Ibom); Direktan Kudi, Maxwell Okoh (Bayelsa); Wakilin Jihar Delta, Prophet Jones Erue; Chief Victor Ekhatar (Edo); Joy Yimebe Nunieh (Rivers); da Nwogu Nwogu (Abia).

DUBA WANNAN: APC ta fallasa wani makirci da Atiku da PDP ke shiryawa alkalan kotun koli

Sauran sun hada da Theodore A. Allison (Bayelsa); Victor Antai (Akwa Ibom); Maurice Effiwatt (Cross River); Olugbenga Elema (Ondo); Uchegbu Chidiebere Kyrian (Imo); Wakiliyar Arewa maso Yamma, Aisha Murtala Muhammed (Kano); Wakilin Arewa maso Gabas, Ardo Zubairu (Adamawa) da Wakilin Kudu maso Yamma, Badmus Mutalib (Lagos).

An aike wasikar ne ga Kwamitin Majalisar kan NDDC domin ta tantance su kana an bukaci Shugaban Majalisar Mista Lawan ya bayar da rahoto kan tantancewar bayan kwanaki bakwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel