Babu laifi a zuwa kasashe, amma a dauki ‘yan kasuwa da masana tsaro - Sani

Babu laifi a zuwa kasashe, amma a dauki ‘yan kasuwa da masana tsaro - Sani

Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas a Najeriya, Shehu Sani, ya fito ya tofa albarkacin bakinsa a game da yawan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari yake yi.

Kwamred Shehu Sani ya bayyana cewa akwai bukatar a samu manyan ‘yan kasuwa da kuma wadanda su ka kware a sha’anin tsaro a cikin tawagar da ke bin shugaba Buhari duk inda za shi.

Tsohon ‘dan majalisar ya yi wannan kira ne a shafinsa na Tuwita a safiyar Litinin, 28 ga Watan Oktoba, 2019. Hakan na zuwa ne bayan an sanar da cewa shugaban kasar zai tafi kasar Saudi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Rasha kenan sai aka ji cewa zai sake tafiya zuwa Saudi Arabia. Bayan taron da za ayi a Saudi, shugaban zai tafi Ingila na wasu kwanaki.

KU KARANTA: Buhari zai shilla Saudiyya domin taro da aikin Umrah

Buhari ya tafi taron da aka yi a Kasar Rasha ne da wasu gwamnoni uku; Inuwa Yahaya, Kayode Fayemi, Bello Mutawalle. A tawagar kuma akwai wasu Ministoci da shugaban kamfanin NNPC.

Haka zalika yanzu shugaba Buhari ya tafi Saudiyya ne da wasu gwamnoni; Babagana Zulum, Abubakar Bagudu and Aminu Masari kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana jiya.

Sauran wadanda aka yi tafiyar da su sun hada da Ministoci; Zubairu Dada; Niyi Adebayo; Timipre; Dr. Isa Pantami. Sai kuma NSA, Babagana Monguno da Ahmed Rufa’i Abubakar na hukumar NIA.

Babu laifi don shugaban kasa ya yi tafiyar da za ta kawo mana cigaban tattalin arziki ko kuma shawo kan matsalar tsaro; Sai dai ya kamata mu ga ‘Yan kasuwa ne da Masana tsaro a Tawagar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel