Rufe iyakoki: Nan ba da dade wa ba 'yan Najeriya za su fara yabawa Buhari - Dan Majalisa

Rufe iyakoki: Nan ba da dade wa ba 'yan Najeriya za su fara yabawa Buhari - Dan Majalisa

Dan majalisar jihar Legas, Victor Akande ya ce nan gaba 'yan Najeriya za su yabawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan rufe iyakokin kasar na kasa da ta yi.

Mista Akande mai wakiltan mazabar Ojo I a majalisar Legas ya yi wannan furucin ne a hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a ranar Talata a Legas.

Dan majalisar, wanda shine shugaban kwamitin shari'a, kare hakin 'dan adam da sauraron korafin Jama'a ya ce rufe iyakokin kasar zai amfani Najeriya a bangarorin tsaro da tattalin arziki.

Mista Akande ya ce: "Yafi zama alheri mu rufe iyakokin kasar mu a halin yanzu da barinsu a bude.

DUBA WANNAN: Kano: Sarkin Karaye ya rushe majalisarsa

"Najeriya ba za su gane amfanin hakan ba a yanzu saboda dan kankanin matsin da za a fusktanta; amma alherin zai biyo baya kuma 'yan Najeriya za su yabawa shugaban kasar.

"Tsaron kasar mu abu ne mai muhimmanci; Idan ba mu dauki wannan matakin yanzu ba, zai yi wahala mu kayyade shige da ficen al'umma da makamai balle har muyi nasara kan yaki da ta'addanci."

Dan majalisar ya roki 'yan Najeriya su cigaban da hakuri da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce rufe iyakokin yana da matukar muhimmanci kan tsaro da tattalin arzikin kasar.

Ya ce, "Ya zama dole mu rufe iyakokin mu don muyi yaki da rashin ayyukan yi a kasar mu. Fifita kayayyakin kasashen ketare fiye da mu na gida yana kawo mana cikas.

"Muna samar wa kasashen ketare ayyuka yayin da matasan mu suna nan suna zaman kashe wando.

"Muddin ba mu fara sayan kayan mu na cikin gida ba, ba za a taba magance matsalar rashin ayyukan yi ba a kasar nan.

"Rufe iyakokin zai sanya mu mayar da hankali kan kasar mu har mu koma noma. 'Yan Najeriya za su yabawa gwamnati daga baya saboda wannan matakin da ta dauka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel