CBN ta fadi matakin da zata dauka a kan asusun masu 'sumoga' da ke bankunan kasar nan

CBN ta fadi matakin da zata dauka a kan asusun masu 'sumoga' da ke bankunan kasar nan

Gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya ce za CBN za ta tabbatar da cewa an rufe asusun ajiya na duk mutanen da aka tabbatar suna sana'r 'sumoga', watau shigo da kaya cikin Najeriya ta haramtattun hanyoyi.

Emefiele ya ce bankin CBN zai tabbatar an rufe bankunan masu wannan sana'a a dukkan bankunan da ke aiki a fadin Najeriya nan bada dadewa ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin jim kadan bayan kammala ganawarsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kafin ya tashi zuwa kasar Saudiyya.

Gwamnan babban bankin ya bayyana cewa rufe iyakokin Najeriya na hanyar kasa ya bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da guraben aiyuka ga matasa da kuma kara bunkasa noman shinkafa da kiwo.

DUBA WANNAN: Tabbas ana tafka badakala a daukar aikin gwamnati - Shugaban ma'aikatan FG

"Idan baku manta ba, mun sha bayyana cewa zamu rufe asusun ajiya na masu sana'ar 'sumoga' ko jibge shinkafar kasar waje a Najeriya, kwanan nan zamu fara hakan," a cewar Emefiel yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa.

Da yake amsa tambaya a kan rufe iyakokin Najeriya na kasa, Emefiele ya ce tun kafin gwamnati ta dauki matakin rufe iyakokin, shugaban kungiyar manoma shinkafa daga jihar Kano ya kira shi domin sanar da shi cewa basa samun ciniki saboda cigaba da shigo da shinkafar kasar waje da ake yi ta iyakokin Najeriya da kasar Benin da Nijar.

Emefiele ya bayyana cewa rufe iyakokin Najeriya na daga cikin matakai masu muhimmanci da gwamnati ta dauka domin inganta tsaro da kuma farfado da tattalin arziki a cikin gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel