UNIMAID: Majalisar dattawa ta hana karin kudin makaranta daga N25,000 zuwa N129,00

UNIMAID: Majalisar dattawa ta hana karin kudin makaranta daga N25,000 zuwa N129,00

Majalisar dattawa ta umurci shugabannin jami'ar Maiduguri su dakatad da shirin karin kudin makarantar dalibai daga N25,000 zuwa N129,000.

A jawbin da hadimin shugaban majalisar dattawa kan yada labarai, Ezrel Tabiowo, ya saki, ya ce majalisar ta umurci kwamitin TETFUND ta gudanar da bincike kan lamarin domin shawo kanshi.

Majalisar ta yanke shawaran sa baki cikin zancen karin kudin makarantan ne bisa kukan da Sanata Abubakar Kyari ya kawo.

Sanata Kyari mai wakiltan Borno ta Arewa ya nuna bacin ransa kan wannan abu da shugabannin jami'ar UNIMAID ke kokarin yi.

Ya ce babban makamin yakan akidar Boko Harama arewa maso gabas da farfado da yankin shine Ilimi. Kashi 62% na kananan yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya na Arewa.

A baya mun kawo muku rahoton cewa Daliban jami'ar Maiduguri na cikin jimami da alhini sakamokon tashin gwauron zabi da kudin makarantarsu yayi.

KU KARANTA: Idan kuka lura za ku ga cewa mun zabi shugabanni Jahilai - Sarkin Kano

A ranar Talatar makon jiya, hukumar gudanarwar jami'ar Maiduguri ta fidda sabon jadawalin kudin makarantar daliban makarantar.

A zangon da ya shude, sabbin dalibai na biyan daga N30,000 zuwa N40,000 ne. Amma sabon jadawalin yanzu haka na nuna zasu biya daga kan N100,000 zuwa N200,000.

Daliban da zasu karanci fannin likitanci na jami'ar zasu biya N165,000 ne a sabon zangon.

Kashi 70 na daliban jami'ar 'yan asalin jihar Barno ne. Iyayensu na daga cikin wadanda suka rasa muhallinsu a halin yanzu suna sansanin gudun hijira. To da me zasu ji? Karin kudin makarantar ko kuwa rasa matsuguni da suka yi sakamakon rikicin Boko Haram da ya ritsa dasu?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel