MInista ya fado daga mumbari a wani taro

MInista ya fado daga mumbari a wani taro

Ministan tattalin arziki na kasar jamus, Peter Altmaier, ya yi mummunar faduwa a yayin da uake niyyyar sauka daga kan mumbari a wani taron tattalin arziki da ya dogara akan fasahar zamani.

Lamarin ya auku ne bayan da Altamaier ya kammala jawabin bude taron da gwamnatin arewa maso yammacin kasar Dortmund ta dau nauyi.

Wata hadimarsa ta tabbatar da cewa, ubangidannata ya yi tuntuben ne bayan da ya tsallake kafa daya ta mumbarin.

Tuni masana kiwon lafiya suka yi caa akansa don duba halin da yake ciki bayan da suka sa bakin kyalle suka shinge shi daga mutane.

Tuni dakin aka sallami mutane suka fita daga dakin taron.

DUBA WANNAN: CBN ta fadi matakin da zata dauka a kan asusun masu 'sumoga' da ke bankunan kasar nan

Daga bisani kuwa motar daukar marasa lafiya ce ta zo ta kwashi Altmaier zuwa asibiti kamar yadda majiya daga dpa ta sanar.

An tabbatar da cewa yanzu haka ministan yana cikin hayyacinsa kuma tuni ya mika godiyarsa ga likitocin da suka bada gudummawarsu wajen ceto rayuwarsa.

A wani labari kuma da jaridar Legit.ng ta ruwaito kwanaki, kunji yadda wani minista a kasar Vietnam ya fado daga bene, abinda yayi sanadiyyar mutuwar ministan har lahira.

Ministan ya fado ne daga bene mai hawa 8 na ofishinsa yayin da yake shirin tafiya wani taro na ma'aikatar ilimi na ksara.

hakan kuwa ya jawo cece-kuce domin wasu sun zargi cewa ba mutuwar Allah da annabi bace. Tuni jami'an tsaro suka bazama don gano yadda abin ya kasance tare da lakwarin bankado duk wata munakisa da ka iya zama ajalin ministan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel