Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Ekweremadu, Abba Moro da Ifeanyi Uba

Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Ekweremadu, Abba Moro da Ifeanyi Uba

Kotun daukaka kara da ke zama a Makurdi, babbar birnin jihar Benue a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba, ta tabbatar da zaben Abba Moro a matsayin sanata mai wakiltan Benue ta kudu a majalisar dattawa.

Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Steve Lawani ya tunkari kotun daukaka karan bayan kotun zabe ta yi watsi da shari’ansa akan rashin inganci.

Da yake zartar da hukunci, kotun daukaka karan karkashin jagoranci, Justis Jumai Sankey, ya jaddada hukuncin kotun zaben.

Moro, tsohon ministan cikin gida, ya yi takarar zabe a karkashin inuwar jam’iyyar Democratic Party (PDP).

A kotun daukaka kara reshen jihar Enugu, an tabbatar da zaben tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu.

Ekweremadu wanda ya yi takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, na wakiltan yankin EEnugu ta yamma.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsige dan majalisa na APC a Kogi, ta yi umurnin sake sabo zabe

Da yake yanke hukunci kwamitin kotun kakashin jagorancin Justis I.M. Salawu, ya yi watsi da karar da Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu ta APC ta daukaka kan rashin inganci.

Kotun daukaka karan da ke zama a Enugu ya kuma tabbatar da nasarar zaben Ifeanyi Ubah a matsayin sanata mai wakiltan Anambra ta kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel