Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsige dan majalisa na APC a Kogi, ta yi umurnin sake sabo zabe

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsige dan majalisa na APC a Kogi, ta yi umurnin sake sabo zabe

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta sallami dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Ajaokuta da ke jihar Kogi, Mohammed Lawal.

Lawal wanda ya kasance mamba na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya yi nasara da farko a karar da aka shigar kotun zabe a jihar.

Da take zatar da hukunci, kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta sake gudanar da sabon zabe a rumfunar zabe 21 da ke mazabar.

Dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aloysius Okino ne ya daukaka kara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi wasu manyan nade-nade masu muhimmanci

Hukuncin na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan kotun koli ta tsige mamba na APC mai wakiltan Lokoja/Kogi a majalisar wakilai sannan ta kaddamar da Barista Shaba Isah Ibrahim na PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.

A wani labari makamancin haka mun ji cewa Kotun daukaka kara da ke zamanta a Enugu ta yanke hukuncin cewa Honarabul Obinna Chidoka ne hallastacen zababben dan majalisar tarayya mai wakiltan Idemili ta Arewa da Kudu a majalisar dokoki na tarayya.

Kotun da soke nasarar dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Ibezi Ifeanyichukwu da Hukumar Zabe ta kasa INEC ta sanar a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 23 ga watan Fabrairu a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n

Source: Legit Nigeria

Online view pixel