Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan IPOB da yan sanda, an kusa kashe DPO

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan IPOB da yan sanda, an kusa kashe DPO

DPO na ofishin yan sandan Kpirikpiri a jihar Ebonyi, John John, ya tsallake rijiya da baya a yammacin Lahadi yayinda wasu yan kungiyar yakin neman Biyafara suka baiwa hammata iska a jihar. Cewar hukumar.

Rikicin ya barke ne a makarantar firamaren Oguzoronweya dake karamar hukumar Ebonyi.

Yan sanda sun dira wajen da yan kungiyar IPOB suke ganawa domin tarwatsasu saboda haramtacciyar kungiya ce a Najeriya.

Kawai sai suka kaiwa DPO John John hari inda suka rika jifanshi da duwatsu.

Jami'an yan sanda sun damke wani lauya mai sune Orogwu Ndubuisi, da budurwarsa saboda na gansu tare da yan kungiyar suna ganawa.

KU KARANTA: Idan kuka lura za ku ga cewa mun zabi shugabanni Jahilai - Sarkin Kano

Hakazalika an damke yan kungiyar biyar yayinda sauran suka arce.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Loveth Odah, ta ce yan kungiyar suka fara jifan yan sanda daga ganinsu.

Ta ce DPO John ya sha da kyar saboda ya sanya hular kwano.

Tace: "Me yasa suke cewa yan sanda sun far musu wajen ganawa? Shin ya kamata su rika wani taro a Najeriya bayan an haramta kungiyar? A doka, wannan taron haramun ne,"

"Baccin dan sandan ya sanya kayan kare kansa da hulan kwano , da sun kashe shi. Da yanzu kun samu labarin cewa an kashe CSP."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel