Yan majalisar dokokin Edo sun ruga wajen Buhari domin neman ceto daga hannun Obaseki

Yan majalisar dokokin Edo sun ruga wajen Buhari domin neman ceto daga hannun Obaseki

Kimanin zababbun mambobin majalisar dokokin jihar Edo 14 da ba a rantsar ba har yanzu ne suka mika kokon bararsu a gaban Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ya sanya baki sannan ya saita gwamnan jihar, Godwin Obaseki.

Yan majalisar sun bayyana cewa basu ji dadin yadda rikicin siyasa ke kunno kai a majalisar dokokin jihar ba.

Channels Television ta ruwaito cewa har yanzu ba a rantsar da mambobin majalisar ba duk da nasarar da suka yi a zaben.

Wani jigo a cikin fusatattun yan majalisar kuma mamba da ya kamata ya wakilci mazabar Uhunmwode, Washington Osifo, ya fada ma manema labarai cewa akwai bukatar Shugaban kasar ya gaggauta sanya baki a lamarin.

Sun zargi gwamnan da kai su bango sannan sun zarge shi da sanya damokradiyya cikin hatsari. A gare su, idan har Buhari ya sanya baki toh hakan zai kawo karshe halin da ake ciki a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi wasu manyan nade-nade masu muhimmanci

Osifo ya zargi Obaseki da gudanar da ayyukan da suka saba ma tsarin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta hanyar rantsar da yan majalisa 10 kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel