Gwamnati ta bayyana matakin da za ta dauka a kan masu yada labaran kanzon kurege

Gwamnati ta bayyana matakin da za ta dauka a kan masu yada labaran kanzon kurege

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yawaitan samun labaran kanzon kurege da maganganun batanci ka iya kunna wutar rikici a kasar nan idan har ba matakin gaggawa aka dauka a kan haka ba.

Ministan labarai, Lai Muhammad ne ya bayyana haka a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba yayin da yake tattaunawa da manema labaru a garin Abuja, inda yace gwamnati ba za ta lamunci watsa labaran karya ba, don haka za ta saka kafar wando daya da duk mai irin wanna dabi’a.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Hukumar kwastam ta kama sundukai 32 makare da shinkafar kasar waje fal!

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito Ministan yana cewa: “Akwai hadari sosai a tattare da labaran karya da maganganun batanci wanda ka iya kawo tangarda ga tsarin mulkin dimukradiyya da kuma hadin kan kasa, daga karshe ya zamto barazana ga cigaban zaman Najeriya a matsayin kasa daya al’umma daya.

“Babu wata gwamnati da zata zura idanu ta bari labaran kanzon kurege da karairayi su mamaye kafafen sadarwarta saboda hadarin dake tattare da hakan wajen kunna rikici tare da ruruwa bambamce bambamcen dake tsakaninmu da tayar da rikici a kasar.

“Wannan yasa dole ne mu cigaba da lalubo hanyoyin magance wanzuwar labaran karya da maganganun batanci a tsakaninmu har sai mun kawar dasu daga cikinmu.” Inji shi.

Daga karshe, minista Lai ya yi kira ga yan jaridu da su baiwa gwamnati goyon baya bisa kokarin da take yi wajen kawo karshen labaran karya da maganganun batanci musamman a kafafen watsa labaran kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel