Da dumi dumi: Hukumar kwastam ta kama sundukai 32 makare da shinkafar kasar waje fal!

Da dumi dumi: Hukumar kwastam ta kama sundukai 32 makare da shinkafar kasar waje fal!

Jami’an hukumar yaki da fasa kauri, sun samu nasarar cafke wasu manya manyan sundukan daukan kaya guda 32 makare da haramtacciyar shinkafa yar kasar waje a jahar Legas, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an shigo da shinkafar ce ta tashar jiragen ruwa na Tin Island dake Apapa jahar Legas kamar yadda wani jami’in hukumar ya tabbatar. Jami’in ya bayyana cewa shinkafar ta lalace tun a shekarar 2018, kuma daga kasashen China da Thailand aka shigo dasu.

KU KARANTA: Dan bindiga mai shekaru 84 ya bindige Musulmai 2 a Masallacin kasar Faransa

A yayin da yake duba shinkafar, shugaban hukumar kwastma, Hamid Ali, ya bayyana cewa da farko dai shinkafar ta lalace tun a shekarar 2018, amma a cikin wani sunduki na daban, ya ga an cika wasu buhuhuna dauke da sabon ranar da shinkafar za ta lalace, wanda hakan ke nufin zasu canza musu buhu kenan.

Majiyarmu ta kara da cewa hukumar kwastam ta kama wadannan buhuhunan shinkafa ne kwana daya rak bayan ta kama wasu sundukai guda 5 dauke da rubabbun kifi da sauran kayan abinci da suka lalace a tashar jirgin ruwa ta Apapa.

A wani labarin kuma, akalla mutanen Najeriya miliyan 90 ne ke cikin halin matsanancin talauci inji ministar ma'aikatar ayyukan agaji da kula da ibtila’I, Hajiya Sadiya Umar Faruk, inda tace don haka gwamnati ta yanke shawarar fitar dasu daga cikin wannan kangi.

Sadiya ta bayyana haka ne yayin da take gabatar da kasafin kudin ma’aikatarta na shekarar 2020 a ranar Litinin wanda ya kai naira biliyan 44.21 domin neman sahhalewar majalisar dokokin kasar nan.

Sadiya ta gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai dake kula da yan gudun hijira ne a karkashin jagorancin Mohamemd Jega, inda ta bayyana musu cewa daga cikin ayyukan ma’aikatarta akwai magance sababin dake janyo ibtila’I, takaitashi da kuma kulawa da wadanda ya shafa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel