Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi wasu manyan nade-nade masu muhimmanci

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi wasu manyan nade-nade masu muhimmanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba, ya mika sunan Justis John Tsoho zuwa ga majalisar dattawa domin dubawa da kuma tantance shi a matsayin babban alkalin babbar kotun tarayya.

Buhari ya kuma zabi mai girma Justis Bakwaph Kanyip Shugaban kotun masana’antu na Najeriya.

Hazalika ya aika wa majalisar dattawa zababbun kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) su uku.

Zababbun sun hada da Umar Mukhtar Gajiram (Borno), Dr. Aiaiibo Sinikiem Johnson (Bayelsa) da kuma Raheem Muideen Olalekan (Osun).

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kanto wasikar Buhari a zauren majalisar.

A kan nadin alkalin babbar kotun tarayya, Buhari ya ce: "Kamar yadda yake a sashi 250(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara), don haka ina neman majalisar dattawa ta tabbatar da nadin, mai girma Justis J.T. Tsoho a matsayin babban alkali babbar kotun tarayyar Najeriya."

KU KARANTA KUMA: Matashi ya daura laifi akan yunwa bayan an kama shi yana satar biskiti da lemukan kwalba (hoto)

A kan nadin shugaban kotun masana'antu na kasar, Buhari ya ce: "Kama yadda yake a sashi na 250(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara), don haka ina neman majalisar dattawa ta tabbatar da nadin, mai girma Justis Benedict Bakwaph Kanyip a matsayin shugaban kotun masana'antu na Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel