Babu gudu babu da ja baya a maganar tsarin IPPIS – AGF ya ja layi

Babu gudu babu da ja baya a maganar tsarin IPPIS – AGF ya ja layi

Mun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce wa’adinta na daina biyan duk ma’aikatan da ba su kan tsarin IPPIS a karshen watan Oktoban nan, ya na nan zai fara aiki kamar yadda aka shirya.

Babban Akawun Najeriya, AGF, Ahmed Idris, shi ya bayyana wannan a wani jawabi da ya yi Ranar Litinin, 28 ga Watan Oktoba, 2019. Ahmed Idris ya soki kungiyar nan ta ASUU a jawabin na sa.

Akanta Janar din yake cewa adawar da kungiyar Malaman jami’a, ASUU, su ke yi kan komawa tsarin IPPIS, goyon bayan rashin gaskiya ne. Akantan ya nuna cewa za su takawa ASUU burki.

Idris ya ke cewa IPPIS tsarin gwamnati ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo na biyan albashin duk wani ma’aikaci da ya shiga zuwa karshen watan nan da ake ciki na Oktoba.

A jawabin na sa, AGF din ya ce IPPIS zai taimaka wajen adana kudi sannan kuma zai rage facakar dukiyar gwamnati. Idris yace sauran kungiyoyin jami’a sun shiga tsarin, ASUU ce kurum ta rage.

KU KARANTA: Sanatoci sun ki sauraron karamin Minista wajen aikin kasafin kudi

“Sanannen abu ne a Duniya cewa ma’aikata su na da hakkin a biya su albashi da kudin aikin guminsu. Amma babu inda ma’aikaci yake fadawa Ubangidansa yadda za a biya shi.” Inji AGF.

Ya karasa da cewa: “Saboda kowa ya samu damar shiga cikin tsarin, har yanzu ana aikin. Don haka mu na kira ga duk ma’aikatan jami’a su tabbatar sun shiga cikin wannan manhaja ta IPPIS.”

Mista Idris yace gwamnati ba za ta bar ma’aikatanta su yi abin da su ka ga dama, su na sabawa tsarin aiki ba. Sai dai ASUU ta bakin shugabanta, ta bayyana dalilanta na kin amincewa da shirin.

Biodun Ogunyemi ya ce akwai yaudara a manhajar IPPIS wanda illolinsa sun kera amfaninsa. Ogunyemi yace tsarin zai kawo masu cikas wajen daukar ma’aikatan gaggawa ko na wucin gadi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel