APC ta fallasa wani makirci da Atiku da PDP ke shiryawa alkalan kotun koli

APC ta fallasa wani makirci da Atiku da PDP ke shiryawa alkalan kotun koli

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta yi zargin cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar suna shirin amfani da kafafen watsa labarai na kasahen waje don bata sunan alkalan kotun koli.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kotun na koli a ranar Laraba za ta fara sauraron shari'ar kan karar da Atiku da PDP suka shigar na kallubalantar nasarar shugaban kasa.

Sai dai, Sakataren watsa labarai na kasa na APC, Lanre Isa-Onilu a yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin ya ce zargin jam'iyyar na PDP da Atiku sun fara shirya wata makirci don kawa rudani a kasar bayan yunkurin da su kayi na neman Amurka tayi watsi da nasarar Buhari bai yi wu ba.

DUBA WANNAN: Kano: Sarkin Karaye ya rushe majalisarsa

A cewarsa, an biya wani lauya dan kasar Amurka, Bruce Fein da ya yi aiki da gwamnatin tsohon shugaba Ronald Reagan da ya saba rubutu kan shugabannin kasashen duniya ya yi rubutun batanci kan fanin shari'a ta Najeriya da alkalan kotun koli.

Ya ce, "Ya kamata a sani cewa jam'iyyar PDP ta kwallafa ranta kan yadda farfaganda na janyo rudani a Najeriya tsawon shekaru hudu masu zuwa.

"Wannan ba hamayya bane na siyasa. Wannan cin amanar kasa da wasu wadanda ba su kaunar kasar mu keyi. Ya kamata mu sanar da 'yan Najeriya wannan makircin PDP ke shiryawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel