Matashi ya daura laifi akan yunwa bayan an kama shi yana satar biskiti da lemukan kwalba (hoto)

Matashi ya daura laifi akan yunwa bayan an kama shi yana satar biskiti da lemukan kwalba (hoto)

Rahotanni sun kawo cewa an kama wani matashi dan Najeriya yayinda yake satar biskiti da lemukan kwalba daga wani shagon siyar da kayayyaki a jihar Ribas.

A bisa ga rahotanni da ke yawo a yanar gizo, wani mutum da aka bayyana a matsayin Destiny Asuwuo, dan shekara 25, ya fasa shagon a kewayen Rumuodara, wani yanki na Port-Hacourt.

Sai dai kuma, bayan mammalakin shagon ya kama shi, Asuquo ya roke shi cewar yunwa da kishirwa ne ya tunzura shi har ya fasa shagon.

Ya saci biskiti, lemukan kwalba da cincin mai nama.

Kalli wani hoto na Asuquo da kayayyakin da ya sata a kasa:

Matashi ya daura laifi akan yunwa bayan an kama shi yana satar biskiti da lemukan kwalba (hoto)
Matashi ya daura laifi akan yunwa bayan an kama shi yana satar biskiti da lemukan kwalba (hoto)
Asali: UGC

Da wasu yan kungiyar banga suka cigaba da tambayarsa, Asuwuo wanda ya fito daga jahar Anambra, ya bayyana cewa shi yana aikin gyaran famfo ne kuma sannan cewa tsawon kwanaki biyu yana yawo da yunwa, saboda ya gaza samun aiki.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: APC ta kai kwamitin daukaka karan zaben sanata zuwa gaban NJC

Ya kuma yi ikirarin cewa yana fama da gyambon ciki mai tsanani tsawon kwanaki biyu da ya yi ba abinci.

An mika Asuquo zuwa ga ofishin yan sanda a Rumuodara domin kyakyawar bincike da hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel