Idan kuka lura za ku ga cewa mun zabi shugabanni Jahilai - Sarkin Kano

Idan kuka lura za ku ga cewa mun zabi shugabanni Jahilai - Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, a ranar Asabar ya ce yan Najeriya su tabbatar da cewa sun zabi shugabannin masu ilmi tare da sanin darajar Ilimi.

Sarkin ya ce yan Najeriya sun tafka kura-kurai a baya ta hanyar zaben shugabannin marasa ilimi, kuma saboda haka suka gaza tabbatar da ilimin kwarai bayan sun hau shugabanci.

Sarkin Kano ya bayyana hakan ne a taron yaye dalibai na jami'ar Nile dake Abuja inda yace kada yan Najeriya su sake kuskuren zaben jahilai matsayin shugabanni.

Mai martaba wanda ya samu karramawa daga jami'ar tare da Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya ce gwamnatin tarayya tayi amfani da kudin da take kashewa wajen tallafin man fetur wajen ilmantar da matasan Najeriya.

SHIN KA SAN Rufe Boda: Cikin mako daya, an sayar buhun shinkafan gida guda 500,000 - Gwamnan CBN

Sarkin yace: "Ya kamata mu mayar da hankali kan irin shugabanni da wakilanmu ta bangaren ilimi. Idan kuka lura a kasar nan, mun zabi mutane marasa ilmi."

"Ya kamata mu jaddada sanin irin mutanen da muke zama shugabanni da yan majalisa kuma mu tabbatar da cewa wadanda muka zaba na da ilimi kuma sun san darajar ilimi."

A nasa jawabin, Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya yabawa jami'ar kan lambar yabon da aka bashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel