Wata sabuwa: APC ta kai kwamitin daukaka karan zaben sanata zuwa gaban NJC

Wata sabuwa: APC ta kai kwamitin daukaka karan zaben sanata zuwa gaban NJC

Jam’iyyar All progressives Congress (APC) mai mulki ta kai karar kwamitin saukaka karan zaben sanata na jihar Akwa Ibom zuwa gaban majalisar alkalai na kasa (NJC).

Jam’iyyar ta ce ta yanke hukuncin ne biyo bayan bayyana Albert Akpan a matsayin wanda ya lashe zaben Akwa Ibom ta arewa maso gabas da kwamitin ya yi.

A wani jawabi daga sakataren labaran jam’iyyar na kasa, Lanre Issa-Onilu, APC tace hukuncin ranar 18 ga watan Oktoba da kwamitin ya yanke wanda ya jaddada nasarar dan majalisar ya kasance abun al’ajabi.

Da take nuni ga cewar dan majalisan ya yi takara a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), APC ta ce an zartar da hukuncin ne ta hanyar rashin biyayya ga umurnin shugabar kotun daukaka kara, Justis Zainab Adamu Bulkachuwa.

Issa-Onilu yace yayinda jam’iyyar ba zata lamuncin hada lamura akan batun da hukuncinsa ba, yace sun yi mamakin dalilin da yasa kwamitin zai gabatar da hukunci a madadin wani kwamiti da babu shi.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Rigima ya kaure tsakanin majalisar wakilai da ministar Buhari a wajen kare kasafin kudi

Ya cigaba da gargadin cewa APC za ta cigaba da fafutuka adalci akan hukuncin da take zargin an zartar dashi ba bisa ka’ida ba kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel