Rufe Boda: Cikin mako daya, an sayar buhun shinkafan gida guda 500,000 - Gwamnan CBN

Rufe Boda: Cikin mako daya, an sayar buhun shinkafan gida guda 500,000 - Gwamnan CBN

Cikin mako daya da rufe iyakokin Najeriya, manoma sun sayar da buhun shinkafan gida guda 500,000, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele , ya laburta.

Godwin Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayinda yake hira da manema labarai bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja gabanin tafiyarsa Saudiyya.

Ya ce gabanin rufe bodan, shugaban kungiyar masu sarrafan shinkafa a Najeriya ya kawo masa korafin cewa mambobin kungiyar na kukan cewa akwai buhuhunan shinkafa 500,000 a ajiye babu mai saya.

Saboda haka ya bukaceshi su san abinda zasuyi domin ganin cewa basuyi asara ba.

Gwamnan CBN ya ce mako daya bayan rufe boda, shugaban masu sarrafa shinkafan ya sake kiransa a waya cewa dukkan shinkafan da ke ajiye sun kare, an sayar da su.

KO KA SAN Ida kuka lura za ku ga cewa mun zabi shugabanni Jahilai - Sarkin Kano

Yace: "Kwanakin baya, shugaban masu sarrafa shinkafa ya kira ni yana mai cewa dukkan kamfanonin sarrafa shinkafa na dauke da ton 25,000 na shinkafa a ajiye sakamakon safarar shinkafan da akeyi ta Kotono da wasu iyakoki kuma yana bukatan mu dau mataki a kai."

"Mako daya bayan kulle iyakokin, sai mutumin ya sake kira cewa sun sayar da dukkan shinkafan dake ajiye."

"Bugu da kari, mutane sun biya kudin wani shinkafan tun kan a sarrafa kuma an ce suyi hakuri sai an kammala."

Tun watan Agusta shugaba Buhari ya bada umurnin kulle iyakokin Najeriya saboda safarar kayayyakin abinci da yaki ci yaki cinyewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel