Da duminsa: Kotu da kwace kujerar 'dan majalisar APGA ta bawa 'dan takarar PDP

Da duminsa: Kotu da kwace kujerar 'dan majalisar APGA ta bawa 'dan takarar PDP

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Enugu ta yanke hukuncin cewa Honarabul Obinna Chidoka ne hallastacen zababben dan majalisar tarayya mai wakiltan Idemili ta Arewa da Kudu a majalisar dokoki na tarayya.

Kotun da soke nasarar dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Ibezi Ifeanyichukwu da Hukumar Zabe ta kasa INEC ta sanar a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 23 ga watan Fabrairu a jihar.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta bukaci INEC ta bawa Chidoka takardan shaidan lashe zabe kuma ta kwace wanda ta bawa dan takarar na APGA a baya kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

DUBA WANNAN: 'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba

Obinna, dan shekaru 45 a duniya kani ne ga Cif Osita Chidoka, tsohon ministan sufurin jiragen sama.

Shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan muhalli a majalisa zubi ta takwas. Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Legas.

Shine dan majalisa mafi karancin shekaru a majalisar wakilai na tarayya zubi ta shida daga Yulin 2007 zuwa Yulin 2008.

Nasara da ya samu ya saka magoya bayansa musamman matasa murna a kafafen sada zumunta.

A wani labari mai kama da wannan, Kotun koli a ranar Juma'a 25 ga watan Oktoba ta tabbatar da nasarar Nyesom Ezenwo Wike a matsayin gwamnan jihar Ribas.

Kotun ta yi watsi da karar da jam'iyyar AAC da dan takararta Awara Biokpomabo suka shigar da kallubalantar nasarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel