Ba za mu bawa Gwamna Ortom hakuri ba - Gololo

Ba za mu bawa Gwamna Ortom hakuri ba - Gololo

Kungiyar Fulani Makiyaya ta 'Miyetti Allah Cattle Breeders Association' (MACBAN) ta ce ba za ta taba bawa Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai hakuri ba.

A maimakon hakan, ta bukaci gwamnan ya nemi afuwar ta kan korar 'ya'yan kungiyar da ya yi daga wurin da suka kira 'gidansu na gado a jihar ta Binuwai.'

Mai magana da yawun MACBAN, Gaurus Gololo, a wata hirar wayar tarho da ya yi da The Nation a jiya Litinin kan sakon neman afuwa da wata kungiyar Fulanin mai suna Miyetti Allah Kauta Horre ta fitar na neman afuwan Gwamna Ortom kan kashe-kashen da makiyaya suka yi a jihar, ya ce kamata ya yi su nemi gwamnan ya basu hakuri kan kashe mambobinsu da aka yi da kuma korar su daga gidajen iyaye da kakanninsu a Binuwai.

DUBA WANNAN: 'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba

Gololo, tsohon hadimin Gwamna Ortom a kan harkokin Fulani kafin su bata, ya ce kungiyar Fulanin da suke bawa Gwamna Ortom hakuri ba su da mambobi a jihar Binuwai don a garin Jos na jihar Filato suke.

Ya ce sanarwar da aka fitar na bayar da hakurin yaudara ce kawai kuma hakan ba shi da wata alaka kan matsayar MACBAN.

A yayin da ya ke mayar da martani, Sakataren watsa labarai na gwamnan, Terver Akase ya ce Gwamna Ortom ba zai yi musayar kalamai da Gololo ba tunda sun raba jiha.

Ya ce, "Ba za mu kula Gololo ba.

"Hasali ma Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana cewa ta raba jiha ta shi. Ba ya magana a madadin ta. Saboda haka babu amfani a bashi amsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel