An cafke Kansilan Kaduna bisa zargin awon-gaba da Naira miliyan 11

An cafke Kansilan Kaduna bisa zargin awon-gaba da Naira miliyan 11

A Ranar Talatar nan mu ka samu labarin cewa hukumar EFCC ta shiyyar Kaduna ta cafke Kansilan gundumar Kakuri Hausa a Garin Kakuri, da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Jami’an na EFCC masu yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa sun damke Honarabul Theophilus Madami ne bisa laifin cin wasu kudi da su ka haura Naira miliyan 11.

Zargin da hukumar EFCC ta jefa a kan Kansilan sun hada da tozarta amana da awon gaba da kudin jama’a. Jimilar kudin da ake zarginsa da ci su ne miliyan goma sha daya da dubu tamanin.

Mai girma Theophilus Madami ya samu wani Ibrahim Haruna wanda shi ne shugaban kamfanin Pyramid Supplied Services Limited da ke dillacin harkar taliya da nufin zai ba shi kwangila.

KU KARANTA: Dalilin korar ABU Umar daga Jami'ar ABU Zaria

Honarabul Madami ya bukaci kamfanin na shugaban kamfanin Pyramid Supplied Services Limited su kawo masa taliya ne domin ya raawa mutanensa. Wannan ya faru ne a shekarar 2018.

Mista Ibrahim Haruna ya kawowa Kansilar taliyar Naira miliyan 16.08 inda aka ba shi miliyan 5 kafin ragowar kudin kwangilar su fito. Sai dai har gobe kamfanin ba samu cikon miliyan 11.08 ba.

Shugaban kamfanin Pyramid Supplied Services Limited suna shaidawa hukumar EFCC cewa tun da ya yi amfani da kudinsa ya kawo wannan taliya a Nuwamban 2018, cikon kudinsa ba su fito ba.

Hukumar EFCC na reshen Kaduna sun bayyana cewa su na binciken wannan lamari kamar yadda aka kawo masu kara. Da zarar sun kammala bincike, za su maka wannan Kansila a gaban kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel