“N10, 000 ya sa ABU Zariya ta kori Malam AB Umar ba neman mata ba”

“N10, 000 ya sa ABU Zariya ta kori Malam AB Umar ba neman mata ba”

Wasu sababbin bayanai su na zuwa mana cewa ashe kudi N10, 000 ne su kayi sanadiyyar da AB Umar ya bar aiki a jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya shekarun baya da su ka wuce.

Yanzu haka dai jami’ar jihar Kaduna ta KASU ta dakatar da AB Umar daga aiki bisa zargin cewa ya na neman ‘Dalibansa ‘yan mata. Daily Trust ta bi diddikin labarin wannan Malamin jami’a.

Jaridar ta samu labari cewa tun farko an sallami Malamin makarantar daga aiki ne a Jami’ar ABU Zariya inda ya baro saboda ya karbi kudi N10, 000 wajen 'Daliba. A dalilin wannan ya rasa aikinsa.

Abin da ya faru shi ne ya nemi N10, 000 daga hannun wata ‘Dalibarsa, ita kuma ta yarda za ta bada amma da bukatar ya ba ta lambar akawun dinsa. Daga nan sai ta aika kudin zuwa bankinsa.”

“Ita kuma wannan ‘Daliba sai ta yi amfani da takardar da ta tura kudin, ta rubuta wasika zuwa ga shugaban jami’an lokacin, Farfesa Abdullahi Mustapha cewa Malami ya bukaci kudi a hannunta.”

KU KARANTA: AB Umar: Yarinyar da ta yi fallasa tace ta na ganin barazana

“Daga nan shugaban jami’ar ya nemi shugaban jami’an tsaron ya binciki lamarin. CSO ya kafa kwamitin bincike, amma aka gaza samun hujjar da ke nuna dalilin da ya sa aka bada kudin.”

“Abin da aka gagara ganewa shi ne ko shin kyauta aka ba Malamin ko kuma tursasa ‘Dalibar yayi. Umar ya fadawa wannan kwamiti cewa ya roki kudin ne saboda Iyalinsa sun shiga wani hali.”

“Malamin ya kare kansa da cewa ba matsawa ‘Dalibar yayi ba domin bai yi mata alkawarin komai ba. Duk da haka kwamitin sun ga laifin Umar amma babu wanda ta jefe shi da zargin lalata."

Majiyar ta ce, a karshe sai dai aka bukaci a kawo karshen aikin Umar a sashen koyar da aikin jarida (ba bangaren Ingilishi da ake fada ba), amma a lokacin ba a same shi da laifin yin lalata ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel