Kasafin kudi: Sanatoci sun ki sauraron Wakilin da Fashola ya aikowa Kwamiti

Kasafin kudi: Sanatoci sun ki sauraron Wakilin da Fashola ya aikowa Kwamiti

A jiya ne mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust cewa kwamitin harkar SDG a majalisar dattawa sun ki sauraron Abubakar Aliyu wanda shi ne karamin Ministan ayyuka da gidaje.

Kwamitin na SDG ya bukaci Minista Babatunde Fashola ya zo gabansu domin ya yi bayani ne amma sai Ministan ya turo Mataimakinsa wanda Majalisar dattawan ba ta gamsu da hakan ba.

ShugabaR wannan kwamiti, Aisha Dahiru Ahmed Binani, ta tubure a kan cewa dole sai Tunde Fashola ya hallara a gabansu domin ya yi masu bayanin abubuwan da su ka shige masu duhu.

Fashola ya tura Abubakar Aliyu ne domin ya kare kasafin ma’aikatar na shekara mai zuwa a gaban majalisar. Bayan hallarar karamin Minista da kimanin karfe 12:00, sai aka juya masa baya.

KU KARANTA: Sanatan PDP ya hakura da siyasa bayan ya sha kasa a kotun zabe

‘Yan kwamitin sun nuna cewa babu abin da za su karba daga hannun Abubakar Aliyu domin babban Ministan su ke son gani a karan kansa kamar yadda su ka rika ganawa da shi a baya.

Sanata Tai Solarin wanda ya na cikin ‘yan wannan kwamiti na SDG ya koka da yadda Ministan ayyuka zai sabawa umarnin Buhari, ya yi tafiya ketare a daidai lokacin da ake aikin kasafin kudi.

Malam Abubakar Aliyu ya yi kokarin yi wa Sanatocin bayani cewa Mai gidansa, Babatunde Fashola, ya bar Najeriya ne bayan ya samu iznin shugaban kasa, amma ba su amince da haka ba.

Sanata Binini ta nuna fushinta ga yadda Ministan zai bar Najeriya bayan an sanar da shi game da zaman. A nan aka yi ta jiran Raji Fashola har karfe 2:00 na rana amma bai samu hallara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel